15 Yuni 2020 - 07:52
Saudiyya : Sai A Ranar Litini Za’a San Makomar Aikin Hajjin Bana

Saudiyya ta ce a gobe Litini ne, zata sanar da duniya halin da ake ciki game da makomar aikin hajjin bana.

(ABNA24.com) Saudiyya ta ce a gobe Litini ne, zata sanar da duniya halin da ake ciki game da makomar aikin hajjin bana.

Mahukuntan kasar dai sun jima suna nazari game da gudanar da aikin hajjin bana, a daidai lokacin da duniya ke fama da annobar cutar Korona.

Ministan harkokin addini na Saudiyyar, Sahib-zada Noor-ul-Haq, ya ce a ranar Litinin ne 15 ga watan Yuni gwamnatin kasar za ta yanke shawara ta karshe game da makomar Hajjin na 2020.


/129